Abdourahamane Tiani ya mika tutar kasar Nijar ga ’yan wasan da za su wakilci Nijar a wasannin Olympic na Paris 2024
2024-07-23 09:47:50 CRI
A jamhuriyyar Nijar, shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, kuma shugaban kasa birgadiye-janar Abdourahamane Tiani ya gana a ranar jiya Litinin 22 ga watan Julin shekarar 2024 da yamma a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai tare da tawagar ’yan wasan Nijar da za su halarci wasannin Olympic na birnin Paris na kasar Faransa.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.