Sin ta fahimci ainihin bukatun kasashen Afirka
2024-07-23 16:15:30 CMG Hausa
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, Sin da Guinea-Bissau sun inganta hadin gwiwa mai amfani a aikace, da raya tattalin arziki mai kiyaye muhalli. Tun daga ci gaba da aikewa da tawagogin ba da talafin likitanci, da kungiyoyin fasaha na aikin gona, da kungiyoyin hadin gwiwar tattalin arziki, zuwa rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa kan raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya tsakanin kasashen biyu, hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban na samar da fa’ida ta zahiri ga jama’ar kasashensu.
A cikin shirinmu na yau, bari mu dubi yadda kasar Sin ke taimakawa kasar Guinea-Bissau a fannin inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da ba da taimakon fasaha da dai sauransu, don inganta jin dadin jama’ar kasar.