logo

HAUSA

Zaftarewar kasa ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 55 a Habasha

2024-07-23 10:54:14 CMG Hausa

Hukumomi a kasar Habasha, sun sanar da mutuwar mutane akalla 55 sanadiyyar zaftarewar kasa a wani yankin kudancin kasar a jiya Litinin, suna gargadin yuwuwar samun karin adadin mamata.

Wata sanarwa daga sashen kula da harkokin yada labarai na yankin Gofa na kasar, ta ruwaito shugaban yankin Dagmawi Zerihun na cewa, an samu sama da gawarwaki 55 daga iftila’in.

A cewarsa, daga cikin wadanda iftila’in ya rutsa da su, akwai mata da yara, yana mai cewa ana ci gaba da aiki haikan domin ceto mutane. (Fa’iza Mustapha)