logo

HAUSA

Macron da Bach sun yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar Olympic

2024-07-23 11:00:52 CMG Hausa

 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban hukumar gudanar da gasar Olympic ta kasa da kasa ko IOC mista Thomas Bach, sun yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar Olympic ta duniya, a lokacin gudanar da gasar Olympic, da ajin gasar ta masu bukatar musamman ko Paralympic, wadda birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci.

Yayin da yake jawabi a bikin bude zaman hukumar ta IOC karo na 142 a Paris, shugaba Macron ya ce Faransa na aiki tukuru tare da IOC don ganin gasar Paris ta zamo lokacin "Zaman lafiya, da gaskiya da kyakkyawan fata". Ya ce "Za a bude gasar kuma za a fara aiwatar da yarjejeniyar”.

A nasa bangare kuwa, mista Bach, ambato akidun gasar Olympic ya yi, wato goyon bayan juna, da daidaito, da martaba darajar daukacin bil adama.

Tun a watan Nuwamban shekarar 2023 ne MDD ta amince da kudurin aiwatar da yarjejeniyar Olympic da Paralympic na birnin Paris, kudurin da ke kira da a tsagaita bude wuta a dukkanin sassan dake fama da tashe tashen hankula, tun daga kwanaki 7 kafin bude gasar ta Olympic ya zuwa kwanaki 7 bayan kammala gasar Paralympic.   (Saminu Alhassan)