Bangarori Daban-Daban Na Falesdinu Sun Kulla “Yarjejeniyar Beijing”
2024-07-23 14:45:37 CMG Hausa
Bangarori 14, ciki har da kungiyoyin Fatah da Hamas na Palasdinu sun gudanar da shawarwari na neman sulhu tsakaninsu daga ranar Lahadi zuwa Talatar nan a birnin Beijing na kasar Sin, har ma sun sa hannu kan Yarjejeniyar Beijing, wadda ke bukatar dinke baraka da wanzar da hadin kan Palasdinawa. (Amina Xu)