Hukumar zaben Rwanda ta tabbatar da nasarar shugaba Kagame
2024-07-23 10:46:40 CMG Hausa
Hukumar zaben kasar Rwanda ta bayyana shugaban kasar mai ci Paul Kagame na jam’iyyar RPF, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar 15 ga watan nan na Yuli, da kaso 99.18 bisa dari na yawan kuri’un da aka kada.
Kaza lika, mista Frank Habineza na jam’iyyar adawa ta Democratic Green Party of Rwanda ya samu kaso 0.5 bisa dari, yayin da dan takarar Indifenda Philippe Mpayimana ya samu kaso 0.32 bisa dari na jimillar kuri’un.
Jam’iyyar RPF ta mista Kagame, da hadakar jam’iyyun dake mara mata baya, sun lashe kujerun majalissar dokoki 37, cikin jimillar 53 dake wakiltar jam’iyyun siyasar kasar da ‘yan takarar Indifenda. (Saminu Alhassan)