logo

HAUSA

Yarjejeniyar Beijing: Mabudin zaman lafiya a Zirin Gaza

2024-07-23 18:32:22 CMG Hausa

A yau Talata ne bangarori daban-daban har 14 ciki har da kungiyoyin Fatah da Hamas, masu rikici da juna a Palasdinu, suka rattaba hannu kan “Yarjejeniyar Beijing” wadda ke da nufin dinke barakar dake akwai a tsakaninsu.

Kamar yadda Bature kan ce “Charity Begins at Home” wato kyakkyawar tarbiyya na farawa ne daga cikin gida. A tarihin duniya da ma bil adama, babu inda muka taba ganin rarrabuwar kawuna ta kawo ci gaba ko zaman lafiya, sai ma karin tashin hankali da tabarbarewar zamantakewa da tattalin arziki. Duk yadda wani ya kai ga son ganin zaman lafiya a Palasdinu, to ba zai taba samuwa ba muddun bangarorin wurin na adawa da juna.

Wacce fa’ida wannan yarjejeniya take da ita?

Tushen maganace matsalar Falasdinu da rikicin dake wakana tsakaninta da Isra’ila, shi ne dinke barakar dake akwai a cikin gida.

A kullum na kan bayyana kasar Sin a matsayin mai hangen nesa, saboda ta kan nemi warware matsala ne tun daga tushe. Kiran wannan taro da kasar Sin ta yi na hada bangarori masu adawa wuri guda domin lalubo bakin zaren rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin, wani muhimmin mataki ne da babu wanda ya yi yunkurin aiwatarwa. Haka kuma, yunkuri ne da zai dora Palasdinu kan turbar zaman lafiya da farfadowa. Hadin kan bangarorin Palasdinu, shi zai ba da damar a rika jinta da murya daya, kazalika, shi ne zai rika toshe duk wani yunkuri na danniya ko cin zali da za a yi mata.

Hakika wannan rana, da wannan yarjejeniya da rawar da Sin ta taka, za su shiga tarihi, kuma al’ummar Palasdinu da yankin Gabas ta Tsakiya da ma na duniya masoya zaman lafiya, za su jinjinawa kasar Sin bisa halin dattako da ta nuna, da kuma yadda take tsayawa kai da fata wajen ganin an kare cikakken ’yancin da muradun dukkan al’ummar duniya.