Nune-nunen kayayyakin ado na azurfa na kabilar Yi
2024-07-23 14:50:05 CMG Hausa
Nune-nunen kayayyakin ado na azurfa na kabilar Yi ke nan da aka gudanar a karo na farko a gundumar Butuo da ke yankin Liangshan mai cin gashin kansa na kabilar Yi dake lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Al’ummar kabilar suna son yin ado da kayayyakin azurfa, kuma gundumar Butuo ta shahara ne da samun kayayyakin ado na azurfa na kabilar Yi, inda kusan ko ina ake iya ganin mata ‘yan kabilar Yi da ke sanye da nau’o’in kayayyakin ado na azurfa.