Xi ya taya Kagame murna bisa sake zabarsa a matsayin shugaban Rwanda
2024-07-23 18:38:43 CMG Hausa
A ranar 23 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Paul Kagame, bisa sake zabarsa a matsayin shugaban kasar Rwanda.
Cikin sakonsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, Rwanda kasa ce dake da alakar zumuncin gargajiya mai kyau da kasar Sin. A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu bunkasuwa cikin sauri, hadin gwiwa a fannoni daban daban ya samu sakamako mai kyau, kana zumuncin gargajiya na ci gaba da zurfafawa. Yana son yin aiki tare da shugaban kasar don kara karfafa amincewar juna a siyasance a tsakanin bangarorin biyu, da fadada da zurfafa hadin gwiwa a aikace a fannoni daban daban, da inganta dangantakar dake tsakanin sassan biyu zuwa wani sabon mataki.(Safiyah Ma)