Xizang ya bunkasa da sauri cikin shekaru 30 da suka gabata
2024-07-23 06:52:51 CMG Hausa
Masu kallonmu, barka da war haka. Cikin shekaru 30 da suka gabata, jihar Xizang (wato Tibet) mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta bunkasa da sauri sakamakon shirin ba da taimako da gwamnatin kasar ta aiwatar.
Bana ake cika shekaru 30 da kaddamar da wannan shiri na ba da taimako, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yin kwaskwarima bisa dukkan fannoni a Xizang.