logo

HAUSA

Tawagar ‘yan wasan Olympics ta kasar Sin ta isa Paris

2024-07-23 10:38:32 CMG Hausa

Tawagar ‘yan wasan kasar Sin a gasar wasannin Olympics, ta isa Paris, babban birnin kasar Faransa, da yammacin jiya Litinin.

‘Yan wasa 405 ne za su wakilci kasar Sin a gasanni 236 da suka shafi wasanni 30, da za su gudana daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga watan Agusta.

Tuni ‘yan wasan kwallon tebur da badminton da ninkaya da kwallon raga na mata, suka isa birnin na Paris.

Kasar Sin ce ta zo ta biyu, bayan kasar Amurka a teburin lambobin yabo yayin gasar wasannin Olympics ta Tokyo ta shekarar 2020, inda ta samu lambobin zinare 38 da na azurfa 32 sai tagulla 19. (Fa’iza Mustapha)