logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya bukaci birnin Tianjin ya inganta ci gaba ta hanyar zurfafa gyare-gyare

2024-07-23 10:31:34 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga birnin Tianjin na arewacin kasar Sin, da ya aiwatar da gyare-gyare, da fadada bude kofa da bunkasa kirkire-kirkire, da kuma ingiza samar da ci gaba ta hanyar zurfafa gyare-gyare.

Li Qiang ya bayyana haka ne yayin rangadin da ya yi a birnin, biyo bayan zama na 3 na kwamitin kolin JKS karo na 20 da aka kammala a baya-bayan nan.

A yankin raya kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, Li ya tattauna da masu bincike da wakilai daga cibiyoyin fasahar harkokin kudi da sabbin kamfanoni masu tasowa, domin fahimtar yadda ake kafa kamfanonin kirkire-kirkire na kawance da aiwatar da sakamakon bincike.

Firaministan ya kuma bukaci a kara zage damtse wajen inganta ci gaba ta kowace fuska a fannonin fasaha da kirkire-kirkire da kirkiro sabbin dandamalin kirkire-kirkiren kimiyya da kyautata matakan jan hankalin masu binciken kimiyya da tallafawa kanana da matsakaitan kamfanonin kimiyya. (Fa’iza Mustapha)