logo

HAUSA

Xi ya aike da wasikar taya murna ga taron kasuwancin makamashi na Sin da Rasha karo na 6

2024-07-23 21:10:48 CMG Hausa

A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron kasuwancin makamashi na Sin da Rasha karo na 6.

Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da kasar Rasha don ci gaba da inganta hadin gwiwar moriyar juna a fannin makamashi, da kiyaye zaman lafiya da juriya a tsarin masana’antar makamashi da tsarin samar da kayayyaki, da ba da gudummawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar masana’antar makamashin duniya mai karfi, da kiyaye muhalli kuma mai kyau.

A wannan rana ma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aike da wasikar taya murna ga taron. (Yahaya)