logo

HAUSA

Biden ya sanar da janyewa daga takarar shugabancin Amurka tare da bayyana goyon baya ga mataimakiyarsa

2024-07-22 10:21:47 CMG Hausa

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da janyewa daga takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyarsa ta Democrat, bayan karuwar ‘ya’yan jam’iyyar dake nuna damuwa, game da ikonsa na lashe zaben, biyowa bayan gazawarsa a mahawarar watan jiya.

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Lahadi, shugaba Biden ya ce "Duk da cewa buri na shi ne na sake tsayawa takara, na gamsu cewa abu mafi dacewa ga jam’iyyata da kasa shi ne na janye takarata, na mayar da hankali ga sauke nauyin dake wuyana na shugabancin kasa a ragowar wa’adi na". Kaza lika, Biden ya ce nan gaba cikin makon nan zai yiwa Amurkawa cikakken jawabi dangane da shawarar da ya yanke.

A wani sakon na daban da ya wallafa a shafin na sa na X, Biden ya ce yana son baiwa mataimakiyarsa Kamala Harris cikakken goyon baya, da tallafi domin ta samu tikitin yiwa jam’iyyar su ta Democratic takarar shugabancin Amurka.  (Saminu Alhassan)