Birnin Paris ya shirya tsaf domin karbar bakuncin gasar Olympics
2024-07-22 11:00:47 CMG Hausa
Mashirya gasar Olympics ta bana wadda za a bude nan da kwanaki 5 a birnin Paris na kasar Faransa, sun ce birnin Paris ya shirya tsaf domin karbar bakuncin wannan gasa, tare da alkawarta tsaftar kogin Seine da ya ratsa arewacin kasar Faransa.
Da yake tsokaci game da hakan yayin taron manema labarai a jiya Lahadi, shugaban kwamitin tsara gasar ta Paris 2024 Tony Estanguet, ya ce "Mun shirya sosai yayin da muka shiga zangon karshe na karbar bakuncin gasar".
Estanguet, ya ce yanzu haka ana gudanar da ‘yan gyare gyaren karshe ne a daukacin wuraren da gasar za ta gudana, kuma dubban ‘yan wasa da jami’ai na ta isa birnin Paris. Kaza lika, yanayin birnin na kara kyautata. Tun daga farkon watan Yuli, ana iya ganin yadda ruwan kogin Seine ya kasance cikin yanayi mai kyau, kuma za a yi amfani da shi yayin bikin bude gasar, da gasar tseren linkaya ta dogon zango, da gasar wasanni 3 a hade; wato gudu, da tseren kekuna da linkaya.
Kogin Seine, zai taka rawar gani a bikin bude gasar, inda ‘yan wasa 6,000 zuwa 7,000 za su hau kwale-kwale 85 a kogin, lamarin da zai kasance irin sa na farko a tarihin gasar Olympics ta lokacin zafi, da za a gudanar da bikin bude gasar a wani wuri sabanin ainihin filin gudanar da gasar.
Mashirya gasar sun ce ana hasashen sayar da tikiti kimanin 300,000 ga ‘yan kallo da za su tsaitsaya a wasu wurare, da bakin kogin na Seine, da kuma karin wasu masu kallo 200,000 ta wasu gidajen kwana dake kusa da wurin. (Saminu Alhassan)