logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kara habaka masana’antar tsimin ruwa

2024-07-22 20:53:40 CMG Hausa

Wakilan CMG sun rawaito daga hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin cewa, a baya-bayan nan, sassa biyar da suka hada da hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin sun fitar da “Ra’ayin jagoranci kan gaggauta raya masana’antar tsimin ruwa”, wanda ya dauki masana’antar tsimin ruwa a matsayin wani muhimmin bangare na sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da tattalin arziki mai kiyaye muhalli, kuma yake sa kaimi ga inganta shi.

Sabon "Ra'ayin jagoranci" da aka fitar ya ba da shawarar kafa tsarin bunkasa masana'antar tsimin ruwa na farko tare da sha’anin masana’antu a matsayin babbar sashe wanda ya kunshi hadin sassan masana'antu, da ilimi, da bincike da aikace-aikace nan da shekarar 2027.

Wannan 'Ra'ayin jagoranci' ya kayyade takamaiman matakan da za su ingiza ci gaban masana'antar tsimin ruwa da habaka fasahohin kirkire-kirkire a cikin masana'antar tsimin ruwa. (Yahaya)