logo

HAUSA

Yadda Ci Gaban Kasar Sin Ke Tasiri A Duniya

2024-07-22 16:17:42 CMG Hausa

Idan muka ce duniya baki daya ta bibiyi sanarwar cikakken zaman taro karo na 3 na kwamitin kolin JKS karo na 20 ba mu yi karya ba. Magoya baya da abokan huldar Sin sun kasa kunne su ji tabbacin labarin kwanciyar hankali da daidaiton tsarin ci gaban kasar, yayin da masu sukar lamirin kasar suka yi ta kokarin gano alamun karuwar matsaloli, da damuwa, ko ma yiwuwar rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin JKS. A karshe dai, magoya baya sun samu dalilan da suka kwantar musu da hankali, kuma masu zagi dole ne su kasance cikin takaici. A bayyane, zaman ya nuna ci gaba a tsarin siyasa, da tattalin arziki da zamantakewa da aka tsara a babban taron JKS karo na 20 da aka gudanar a shekarar 2022. Zaman ya mayar da hankali ne kan al'amuran cikin gida da nufin kammala aikin zamanantarwa bisa tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da gina ingantacciyar hanyar tattalin arziki ta gurguzu da kuma zamanantar da tsarin kasar da iya tafiyar da harkokin mulki.

Mu dubi tsarin kasuwancin duniya na wannan zamani, jimillar kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya kai kusan dalar Amurka tiriliyan 6, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya ga kasashe fiye da 120. Kasar Sin tana da fiye da rabin sabbin motocin lantarki da aka sayar a duk duniya a yau, kuma tana daukar sama da kashi 80 cikin 100 na kayayyakin samar da wutar lantarki bisa hasken rana a duniya. Yana da wuya a yi tunanin kasuwannin duniya na kwamfutoci da na'urorin laturoni, da sinadarai na hada magunguna, da injuna, da motoci, da sauran kayayyaki daban-daban ba tare da tabo rawar da kasar Sin ta taka ba.

Kusan shekaru 100 da suka shige, tsohon shugaban Amurka Franklin D. Roosevelt ya bayyana cewa, “Yadda matsayinmu a tarihi ke cike da haske haka yake da hadari. Ko dai duniya ta karkata zuwa ga ci gaba da hadin kai da wadatar arziki a ko’ina, ko kuma ta rarrabu." Wannan gaskiya ne a shekarun 1930s kuma ba shakka haka lamarin yake a zamaninmu na yau. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne wajen samun nasarar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin saboda hakan na da matukar tasiri ga tattalin arzikin duniya. Kuma wadanda ke yi wa Sin munanan fata harbin kansu kawai suke yi a kafa. (Mohammed Yahaya)