logo

HAUSA

Taron JKS: Kudurin Kara Zurfafa Gyare-gyare Zai Sa Kaimin Aikin Zamanintar Da Sin

2024-07-22 19:11:23 CMG Hausa

Na fara sanin manufar gyare-gyare da bude kofa ta kasar Sin a lokacin da aka yi bikin cikar manufar shekaru 40 da kafuwa a shekarar 2018. Rahotannin da na gani a game da ci gaban da manufar ta kawowa kasar da sauran kasashen da aka yi kawancen ci gaba tare da su, a karkashin tsare-tsare daban-daban kamar na Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), Dandalin Kawance na FOCAC, sun nuna kyakkyawar alkiblar da Sin ta dosa.

Manufar wadda a bana ta cika shekaru 46 da kafuwa ta kara samun tagomashi yayin da zaman taro na uku na Kwamitin Kolin Jam’iyyar Kwaminisanci ta Kasar Sin (JKS) karo na 20 ya amince da kudurin kara zurfafa gyare-gyare don habaka zamanantar da kasar, a birnin Beijing, kwanan nan.

Babban burin da ake neman cimmawa a kokarin da ake na kara zurfafa gyare-gyare, shi ne ci gaba da ingantawa da raya tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da kuma zamanantar tsarin gudanarwa na Sin da karfin iya shugabanci.

Da yake masu magana kan ce “aiki ga mai kare ka”, ana sa ran nan da 2035, Sin za ta kammala gina tattalin arzikin kasuwanci irin na gurguzu mai matukar inganci a dukkan fannoni. Tabbas hakar kasar za ta cimma ruwa bisa yadda ta sha damarar ganin an sauke duk wani nauyi da ya rataya ga samun nasarar kudurin a yayin da Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin za ta yi bikin cikarta shekara 80 da kafuwa a 2029.

Ba kanta kadai take kallo ba, a duk harkokin ci gaba da wayewa irin na zamani mai inganci da babu coge a ciki, kasar Sin tana duba al’ummar duniya a matsayin wadanda za a gudu tare, a tsira tare. Shi ya sa, sanarwar bayan taron JKS ta jaddada cewa, tsarin zamanintar Sin shi ne tsarin bunkasa zaman lafiya a zamanance, domin “a huldar dake tsakanin kasashen waje da kasar Sin, kasar ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da manufar zaman lafiya mai cin gashin kanta, kana ta himmatu wajen inganta al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya," in ji sanarwar.

A aikace, an ga irin kokarin da Sin take yi a manufofinta na bude kofa da zaman lafiyar duniya ta hanyar kai ci gaban tattalin arziki maimakon tayar da husumar yake-yake a kasashe daban-daban da kuma jawo su a jiki su shigo cikinta domin cin moriyar juna. Wannan ya tsayawa kasashen yamma a kahon zuci, shi ya sa duk abin da kasar ta kawo sai an shafa masa kashin kaji ta hanyar kushe manufar bude kofar da kuma yayata farfaganda a kafafen yada labarunsu daban-daban cewa, manufar tana samun koma-baya da rashin karbuwa a duniya.

To sai dai, a gaya musu “kifi na ganin ka mai jar koma”, domin kasar Sin ta ci gaba da rike kambunta na zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya da zama kasar da ta fi yawan cinikin hajjoji a cikin shekaru bakwai a jere, da ci gaban da ta samu na hada-hadar tattalin arzikin cikin gida a rabin farko na bana da ya kai fiye da Yuan tiriliyan 61, wanda ya karu da kashi 5 idan aka dora a sikeli da na bara war haka.

Bisa jajircewar Sin a karkashin shirinta na bude kofa na zamani, ta ci gaba da fadada huldar kasuwanci da kasashen duniya. Kasuwancin da take yi a karkashin hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) ya karu da kashi 7.2, a rabin shekarar 2024.

Bayan haka, Sin ta kara yawan kasashen da take sahale musu shiga cikinta ba tare da biza ba. A tsakanin wata shida na 2024 kacal, a kalla ’yan kasashen waje miliyan 14 suka shigo cikinta, kusan adadin da ya ninka wadanda suke shiga duk shekara.

Wadannan misalai sun isa su nuna karbuwar da manufar bude kofar Sin ke samu tare da fadada damammakin zuba jari ga ’yan kasashen waje a cikinta.

A bisa tsare-tsaren kara zurfafa gyare-gyare da taron JKS ya aminta da su, tabbas ba Sin kadai za ta ci gajiyar wadannan gyare-gyare ba har da sauran kasashen duniya bisa manufarta ta bude kofa, ba kamar masu tsuke kasuwanninsu na shigo da kaya da fadada na fitarwa kamar yadda su Amurka ke yi ba. (Yahuza Abdulrazaq)