logo

HAUSA

Sin za ta kara kaimi wajen shiga tattalin arzikin kasa da kasa

2024-07-22 19:37:07 CMG Hausa

Yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. 

Game da cikakken zama na uku na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da aka gudanar a makon da ya gabata, ta ce, babban burin wannan taro shi ne fadada bude kofar kasar Sin ga kasashen waje. Kasar Sin za ta kara kaimi wajen shiga tattalin arzikin kasa da kasa, da fitar da karin moriya ga duniya.

Ta kara da cewa, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng zai je kasar Faransa a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Xi Jinping, don halartar bikin bude gasar wasannin Olympics karo na 33 da za a gudanar a birnin Paris a ranar 26 ga watan Yuli da kuma gudanar da wasu ayyuka. Kasar Sin na fatan gasar wasannin Olympics ta Paris za ta samu cikakkiyar nasara.

Game da zagaye na biyu na tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, wanda kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa, Mao Ning ta bayyana cewa, game da batun Falasdinu, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan tabbatar da zaman lafiya da adalci. A ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan tabbatar da adalci ga al'ummar Falasdinu don maido da hakkokin al’ummarta kamar yadda doka ta tanada, kuma tana goyon bayan Falasdinu wajen tabbatar da hadin kai da 'yancin kai, da kafa kasa mai cin gashin kanta.

Mao Ning ta kuma ce, bayan taron koli na Astana da aka gudanar a watan Yulin bana, kasar Sin ta karbi ragamar shugabancin kungiyar SCO daga shekarar 2024 zuwa 2025 a hukumance. Kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan hakan, kuma ta kaddamar da aikin shugabancin kasa a dukkan fannoni.

Ban da wannan kuma, game da rikicin Ukraine, ta ce, kamata ya yi Amurka ta yi wani abu a zahiri don warware rikicin a siyasance, maimakon mayar da alhakinta ga kasar Sin.(Safiyah Ma)