Sin ta fitar takardar aiki kan shirin kar a zama na farkon yin amfani da makaman nukiliya a kan juna
2024-07-22 19:40:04 CMG Hausa
A yau ne shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya fitar da “Takardar aiki kan shirin kar a zama na farkon yin amfani da makaman nukiliya a kan juna”, takardar ta bayyana cewa, hanawa da lalata makaman nukiliya baki daya da kuma kafa duniya maras makaman nukiliya suna cikin muradun bai daya na dukkan bil Adama. A cikin takardar, kasar Sin ta ba shawarar karfafawa kasashe biyar masu makaman nukiliya gwiwa da su sa kaimi ga tabbatar da matsayar da aka cimma kan “Yarjejeniyar ba za a fara amfani da makaman nukiliya a kan juna ba” ko kuma fitar da sanarwar siyasa kan hakan, da tsara daftarin yarjejeniyar da ta dace ko bayanan da za su kasance tushen tattaunawa. (Yahaya)