Ministan harkokin wajen Ukraine zai ziyarci Sin
2024-07-22 19:48:18 CMG Hausa
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta sanar yau Litinin cewa, ministan harkokin wajen kasar Ukraine Dmytro Kuleba zai ziyarci kasar Sin, bisa gayyatar da mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi masa. (Yahaya)