logo

HAUSA

Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai kan wuraren ajiyar mai na mayakan Houthi dake Hodeidah a Yemen

2024-07-21 15:51:37 CMG Hausa

A jiya Asabar ne sojojin Isra’ila suka tabbatar da cewa sun yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren da ke da alaka da mayakan Houthi a kasar Yemen, kwana guda bayan da bam daga jirgin sama mara matuki ya kashe wani mutum a Tel Aviv na kasar Isra’ila.

Tashar talabijin ta mayakan Houthi wato al-Masirah ta labarta kungiyar na cewa an kai harin ne kan wasu wuraren ajiyar man fetur da wutar lantarki a birnin Hodeidah da ke gabar tekun Bahar Maliya ta Yemen, kuma ko dai mutane da dama ne suka mutu ko kuma suka jikkata.

Wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce jiragen yakinta sun kai hari kan wuraren da mayakan na Houthi suke ne, a matsayin martani ga daruruwan hare-haren da suka kai wa kasar Isra'ila a 'yan watannin nan.

Sanarwar ta zo ne bayan da babban mai shiga tsakani na Houthi Mohammed Abdulsalam ya ce hare-haren da Isra'ila ke kaiwa ba zai hana mayakan Houthi kai hare-hare kan birane da jiragen ruwa na Isra'ila ba.

A daya bangare kuma, mazauna Hodeidah sun ce daga nesa ana iya ganin bakar hayaki mai kauri da kuma wuta a wurin da lamarin ya faru. Motocin kashe gobara da motocin daukar marasa lafiya sun garzaya wurin da lamarin ya faru yayin da hukumomi suka killace yankin da ke kusa da tekun Bahar Maliya.

Hukumomin lafiya na yankin ba su bayyana ainihin adadin wadanda suka mutu ba kawo yanzu, a cewa tashar talabijin na Houthi. (Yahaya)