Jakadar Sin a Nijar ya halarci bikin bude gasar dambe ta Nijar karo na 6
2024-07-21 18:06:42 CMG Hausa
A ranar 20 ga watan Yuli, jakadan kasar Sin a Nijar Jiang Feng ya halarci bikin bude gasar dambe ta kasa ta Nijar karo na 6.
Jiang Feng ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, wasan dambe na kasar Sin ya zaburar da al'ummomin kasar Sin da su ci gaba da kokarin tabbatar da 'yancin kai, da farfadowa da neman wadata ga al'ummar kasar Sin, wanda ya dace da inganta kai da ruhin kishin kasa na jama'ar Nijar. A shekarun baya-bayan nan dai wasan dambe ya yi fice a Nijar. Kasar Sin a shirye take ta yi amfani da wasan damben a matsayin wata gada don karfafa mu'amalar al'adu da fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu, da kuma kulla alaka mai karfi tsakanin Sin da Nijar. (Yahaya)