logo

HAUSA

Kasar Sin tana amfani da tsarin inshora wajen kula da dattawa

2024-07-21 15:45:00 CMG Hausa

 

Yau za mu tattauna batun kula da dattawa. Ba a rasa tsoffin mutane a cikin iyali. Saboda haka, yadda za a iya kula da dattawa da kyau, ya shafi damar samun jituwa da ci gaba a zamantakewar al'umma.

Zuwa karshen shekarar 2022, yawan tsoffi a kasar Sin, wadanda shekarunsu sun kai 60 ko fiye, ya riga ya wuce miliyan 280, kwatankwacin kashi 19.8% na yawan al'ummar kasar. Sai dai wace dabara ce kasar Sin ta dauka don kula da dimbin dattawa a kasar? (Bello Wang)