logo

HAUSA

An kaddamar da shirin rabon kayayyakin aikin gona na buliyoyin naira ga manoma a jihar Yobe

2024-07-21 14:33:33 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da rabon kayan aikin gona da suka hada da motocin noma na tsabar kudin naira buliyan 15 da gwamnatin jihar Yobe ta sayo domin rabawa ga manoman jihar.

Yayin bikin da aka gudanar jiya Asabar 20 ga wata a garin Damaturu fadar gwamantin jihar, sanata Kashim Shettima ya ce hakika shirin samar da kayan aikin gonar mataki ne babban da zai taimaka wajen noma wadataccen abinci tare da samar da aikin yi .

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya yabawa gwamnatin jihar Yobe bisa wannan namijin kokarin, ya kuma kara jaddada aniyar gwamnati na habaka sha`anin noma da fadada hanyoyin samar da aikin yi.

Yace abinci shi ne garkuwa wajen tabbatar da al`umma mai zaune cikin zaman lafiya, kuma shi ne ginshikin ginuwar lafiyar bil`adama da daidaituwar tattalin arzikin kowacce kasa.

“Babu wata hanya da za mu bi wajen cimma manyan manufofin mu kama daga mataki jiha zuwa na kasa har sai mun taimaka tare da karfafa gwiwar manoman mu ta hanyar tabbatar da ganin suna da kayan aiki na zamani da kuma ilimin yadda za su cimma burin su na noma amfanin gona mai yawa”

A jawabin sa gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce sanin kowa cewa jihar Yobe na daya daga cikin jahohin da suka tsinci kansu cikin kalubalen tsaro, wanda wannan ya taka rawa wajen hana manoman jihar iya zuwa gonakin domin yin noma, baya ga haka kuma jihar na fuskantar matsalolin muhalli kamar zaizayar kasa da kwararowar Hamada.

“Amma duk da wadannan kalubale aikin gona shi ne mafi rinjayen sana`ar al`ummar jihar suka fi karfi a kai, kuma a bisa cigaba da aka samu wajen zaman lafiya a jihar, yanzu haka dukkan gonakin jihar manoma na iya zuwa domin aikata su, wannan ce ta ba mu damar samar da wadannan kayayyakin aikin gona domin raba su ga kowanne sashe na jihar domin amfanin kanana da matsakantan manoman dake fadin jihar.(Garba Abdullahi Bagwai)