logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane 8 a lardin Sichuan na Sin

2024-07-21 15:01:16 CMG Hausa

A yau Lahadi da karfe 1 na safe agogon kasar Sin, gwamnatin gundumar Hanyuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru, inda ta ba da rahoto kan halin da ake ciki a fannin aikin ceto bayan abkuwar bala'in ambaliyar ruwa a wani kauyen gundumar jiya Asabar. An ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa sama da mutane 30 ne suka bace sakamakon bala'in. Sa'an nan ya zuwa karfe 10 na daren jiya, an gano gawarwakin mutane 8. Baya ga haka an kwashe mutane 412 zuwa wuri mai tsaro, da samar da jinya ga wasu 12 da suka samu raunuka.

An ce da misalin karfe 2 da minti 30 na safiyar jiya Asabar, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a kauyen Xinhua, na gundumar Hanyuan, lamarin da ya lalata hanyoyin sadarwa, da hanyoyin mota, da gadojin wurin. Daga bisani nan take karamar hukumar wurin ta kaddamar da ayyukan ceto, inda ta tura tawagogi 23 masu kunshe da ma'aikatan ceto sama da 1,000, zuwa wurin da bala'in ya abku, gami da jibge kayayyakin aiki sama da 1,500, kamarsu jiragen sama marasa matuka, da injunan hakar kasa, da gadoji na gaggawa, da motocin sadarwa a can, inda ake gudanar da ayyukan neman mutanen da suka bace, da sake tsugunar da jama'ar da bala'in ya ritsa da su, da dai sauransu.

A sa'i daya kuma, gwamnatin birnin Ya'an na lardin Sichuan cikin gaggawa ta ware tantuna 500, da barguna 3,500, da gadaje masu lankwasa 3,500, da dimbin fitilu, don a kai su wurin da bala'in ya abku. A halin yanzu, an dawo da hidimar sadarwa, da ayyukan hanyoyin sufuri a wurin, kuma a hankali ana maido da wutar lantarki. (Bello Wang)