logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya bukaci sassan kasa da kasa da su bunkasa hadin gwiwa tare da kungiyar SCO

2024-07-20 16:05:34 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa tare da kungiyar hadin kai ta Shanghai ko SCO, wajen wanzar da zaman lafiya da tsaron duniya.

Fu Cong, ya yi tsokacin ne yayin mahawarar da aka gudanar a zauren kwamitin tsaron MDD a jiya Juma’a, game da bukatar hada karfi da karfe tsakanin MDD da kungiyoyin shiyyoyi, inda ya ce, kungiyar SCO ta yi rawar gani a fannin shawo kan kalubalolin duniya, da yayata tasirin sassan duniya daban daban, da raya tattalin arzikin duniya mai game dukkanin bangarori.

Jami’in ya kuma jaddada bukatar aiwatar da matakai madaidaita da nufin ingiza tasirin sassan duniya daban daban, da bunkasa tattalin arzikin duniya mai game dukkanin bangarori, ta yadda za a kai ga shawo kan batutuwa masu sarkakiya dake addabar sassan kasa da kasa.

Fu Cong, ya ce ya zama wajibi a aiwatar da salon cudanyar dukkanin sassa bisa gaskiya, karkashin ka’idojin MDD, da karfafa tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar SCO, ta yadda za a karfafa yunkurin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya tsakanin kasa da kasa.    (Saminu Alhassan)