logo

HAUSA

Wane tasiri sabbin karfin ci gaban kasar Sin za su yi ga duniya?

2024-07-20 21:11:08 CMG Hausa

A halin da ake ciki, “Sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko”, ya zamo jumlar da ake yawan ji a fannin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. Cikakken zaman 3 na kwamitin kolin JKS na karo na 20, wanda aka kammala a baya-bayan nan, ya fitar da matakan zurfafa sauye-sauye a dukkanin fannoni, wanda hakan ke bukatar kyautata tsari, da dabarun raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, daidai da halayen da ake ciki a gida.

Masu fashin baki sun yi amannar cewa, wannan mataki na nuna irin dagewar kasar Sin, a fannin zurfafa sauye-sauye masu alaka da samar da tsari na shukawa, da bunkasawa, da rayawa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, ta yadda za a kara azama kan cimma nasarar samun bunkasuwa mai inganci, da ingiza salon zamanantarwa irin ta Sin.

Tsohon mataimakin babban sakataren MDD Erik Solheim, ya jinjinawa kokarin kasar Sin na zurfafa sauye-sauye, da kara azamar raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko. Ya yi imanin cewa, amfani da kimiyya da fasaha a matsayin jagora, da nacewa neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, su ne jigon nasarar kasar Sin a wannan karni na 21.

A matsayinta na kasuwa ta daya a duniya a fannin cinikayyar makamashi mai tsafta, da sarrafa kayayyakin aikin masana’antu, Sin ta ci gaba da samarwa duniya hajoji masu matukar inganci, kana ta karfafa cimma nasarar sauyin da duniya ke yi zuwa ga ayyuka marasa gurbata muhalli, da masu fitar da karancin iskar carbon. A baya-bayan nan, an yi nasarar sanya hannu kan kwangilar aikin adana makamashi mafi girma a duniya, tsakanin katafaren kamfanin sabon makamashi na kasar Sin wato Sungrow da kamfanin Algihaz na kasar Saudiyya, wanda hakan ke dada nuni ga yadda ci gaba mai inganci na kasar Sin ke amfanar da duniya baki daya.

Abu ne a zahiri, cewa yayin da Sin ke kara zurfafa sauye-sauye a dukkanin fannoni, sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko zai kara zaburar da bunkasuwa, da yaukaka ci gaba mai inganci, da salon Sin na zamanantarwa, da ingiza sabon karsashi ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.  (Saminu Alhassan)