Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce Najeriya na kokarin yin fice a bangaren hakar ma’adinai a tsakanin kasashen Afrika
2024-07-20 17:11:18 CMG Hausa
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana aikin kokarin ganin Najeriya ta kasance ja gaba a fagen sha’anin hakar ma’adinai a tsakanin kasashen dake nahiyar Afrika.
Ya bayyana hakan ne ranar larabar 17 ga wata a birnin Abuja yayin babban taron kasashen Afrika kan batun albarkatun kasa da harkokin saka jari a bangaren makamashi na 2024, ya tabbatar da cewa, tuni aka yi nisa wajen cimma wannan mataki ta hanyar bayar da dama ga masu zuba jari ‘yan kasa da na kasashen waje.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya wakilci shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen taron da ya samu halartar ministocin ma’aikatun kula da ma’adinai na kasashen Afrika, ya ce Najeriya ita ce kan gaba a jerin kasashen dake nahiyar Afrika da suke da ma’adinai daban daban.
Ya ce taron wanda aka shirya shi husasan domin karfafa tsarin saka jari a bangaren ma’adinan kasa da kyautata muhalli ya zo daidai da lokacin da duniya ke fadada kafofin tattalin arziki domin samun kudaden musaya masu yawa, maimakon dogaro dai a kan albarkatun man fetur.
Sanata Kashim Shettima ya ci gaba da cewa kasashen dake nahiyar Afrika suna da albarkatu nau’ika daban daban, inda ya yi fatan cewa taron zai bude musu kofa da za su kara samun dabarun yadda za su rinka alkinta su, tare kuma da sanin hanyoyin zamani da za su tabbatar da muhalli mai inganci domin bunkasar lafiyar al’ummar dake nahiyar.
“Ina tabbatar muku cewa wannan gwamnati za ta ci gaba da yin aiki tare da kasashen duniya musamman kasashen Afrika da muke makwabtaka da su ta hanyar kirkirar tsarin safara ta kan iyakoki, ta yadda za a rinka fitar da kaya cikin sauki zuwa daukacin kasashen dake nahiyar, haka kuma wannan zai bayar da damar cin moriyar tsarin hada-hadar kasuwanci mara shinge a tsakanin kasashen.”(Garba Abdullahi Bagwai)