Beijing: Peng Liyuan ta halarci sansanin yaran Sin da Afirka
2024-07-20 15:57:20 CMG Hausa
Mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta halarci sansanin yaran Sin da nahiyar Afirka na lokacin zafi a jiya Juma’a a nan birnin Beijing. Cikin jawabin da ta gabatar a sansanin, mai lakabin "Kauna a hasken rana", Peng Liyuan ta ce, sansanin ba kawai dandalin taruwar yaran Sin da na Afirka ba ne, har ma alama ce dake tabbatar da kusancin dake akwai tsakanin sassan biyu.
Ta ce, al’ummun Sin da na nahiyar Afirka har kullum suna fahimta da goyon bayan juna, a turbarsu ta neman samun farin ciki. Kaza lika, a matsayinta na kawar Afirka a turbar neman ci gaba, Sin ba kawai ta mayar da hankali ga tabbatar da samun ci gaba mai inganci ba ne, har ma tana samar da gudummawar ingiza managarcin salon ci gaban yaran nahiyar Afirka.
Daga nan sai ta tabbatar da aniyar sassan biyu, ta wanzar da sahihin kawance, da fatan daukacin yaran nahiyar Afirka da suka halarci wannan sansani, za su zamo jakadun yada kawancen gargajiya tsakanin Sin da Afirka, kuma sabon karfin gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya. (Saminu Alhassan)