logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kaddamar da biranen gwajin amfani da tsarin taswira na tauraron dan adam na BeiDou

2024-07-19 11:46:50 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da masana’atu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce kasar na shirin mara baya ga fadada amfani da tsarin taswira na tauraron dan adam na BeiDou.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce ana shirin ware wasu birane da za su kasance na gwaji, domin amfani da tsarin BeiDou a bangarorin da suka hada da kayayyaki da hidimomin bukatun jama’a da kere-kere da kuma bangarori masu tasowa kamar na kirkirarriyar basira (AI).

A bangaren kayayyaki da hidimomin bukatun jama’a, biranen za su mayar da hankali kan bangarori kamar na wayoyin salula da na’urorin da ake daurawa ko sakawa a jiki da wadanda ake rikewa a hannu da kayayyakin bulaguro da mutane daban-daban ke amfani da su da jirage marasa matuka da ba sa yin nisa. Za kuma a karfafawa kamfanoni gwiwar samarwa da kera kayayyaki masu amfani da tsarin na BeiDou, lamarin da zai inganta tsarin samar da kayayyaki.

A bangaren kere keren kayayyaki kuwa, biranen za su gaggauta amfani da BeiDou a muhimman bangarori kamar na motoci da jiragen ruwa da jiragen sama da mutum-mutumin inji. (Fa’iza Mustapha)