logo

HAUSA

Sabbin hukumomin Nijar sun dauki niyyar rage farashin man fetur

2024-07-19 10:15:34 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, sabbin hukumomin soja a karkashin jagorancin shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, shugaban kasa, birgadiye janar Abdourahamane Tiani, sun sanar da matakin rage kudin man fetur daga dukkan fadin kasar Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada, ya aiko mana da wannan rahoto. 

Shi dai wannan babban albishir da ’yan kasar Nijar suka wayi gari da shi, ya jima da ’yan kasar din suke dakonsa tun ma lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou har ma ya zo ga mulkin tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum amma hakan ba ta samu ba, sai ga shi kamar daga sama wannan albishir ya fito a yayin zaman taron ministoci na baya bayan nan a karkashin jagorancin shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP. Kamar yadda mambobin kwamitin ceton kasa da gwamnatin faraminista Ali Mahamane Lamine Zeine suka yi ma ’yan kasa alkawari, shugaban kasa Abdourahamane Tiani, ya dauki matakin rage kudin man fetur a gidajen saida mai daga dari da takwas kudin sefa (540 Fcfa) zuwa dari ba tamma guda kudin sefa (499 Fcfa), kuma wannan farashi zai fara aiki a dukkan fadin kasar Nijar daga bakin ranar 23 ga watan Julin shekarar 2024, a cewar sanarwar taron ministocin da gidan rediyo da talabijin na kasa RTN suka rawaito. Haka kuma wannan zai shafi ma farashin man gazuwal zai rage daga bakin wannan rana zuwa dari da ishirin da dala hudu ba tamma 2 kudin sefa (618 Fcfa).

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.