Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu 70 a matsayin sabon tsarin mafi kankantar albashi ga ma’aikatan kasar
2024-07-19 10:06:22 CMG Hausa
Da yammacin jiya Alhamis ne 18 ga wata shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu saba’in a matsayin sabon tsarin mafi kankantar albashi ga ma’aikatan kasar.
Ya sanar da hakan ne yayin taronsa da shugabancin kungiyar kwadago kasar a fadarsa dake birnin Abuja, ya kuma yi alkawarin cewa a duk shekaru uku za a rinka sabunta dokar sabon tsarin albashin.
Daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Daman dai tun a makon jiya ne aka sanar cewa shugaban zai sake zama karo na biyu da ’yan kungiyar kwadagon domin dai fitar da matsayar karshe a kan batun sabon tsarin albashin bayan tashi a zaman farko ba tare da an cimma yarjejeniya ba.
A zaman na jiya Alhamis dai, dukkan bangarori biyu bakinsu ya zo daya na tsayar da naira dubu 70 a matsayin mafi kankantar albashin sabanin naira dubu 62 da tun farko gwamnati ta yi wa ’yan kungiyar kwadagon ta yi.
A sakamakon wanann ci gaba ne, yanzu shugaban na tarayyar Najeriya zai mika kudurin dokar albashin ga majalissar dokokin kasar a makon gobe domin samun amincewarta ta yadda za ta zama doka. (Garba Abdullahi Bagwai)