logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da asusun bayar da rancen kudin karatu ga daliban kasar

2024-07-19 14:23:28 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin asusun bayar da rancen karatu ga daliban kasar.

Yayin bikin kaddamar da asusun a hukumance ranar Laraba 17 ga wata a fadar sa dake birnin Abuja, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yin bakin kokari wajen samar da isassun kudade domin tabbatar da dorewar shirin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Shugaban na taryyar Najeriya ya bayyana ilimi a matsayin baban makami na yakar talauci, ayyukan ta’addanci da kuma sauran miyagun laifuka a cikin al’umma, a don haka gwamnati ba za ta taba daukar wannan shiri da wasa ba.

Ya ce, daliban Najeriya suna matukar bukatar agajin karatu domin su samu damar cimma burinsu na kasancewa masu matukar tasiri ga ci gaban kasa a dukkannin fannoni.

“Ilimi babban makami ne na fatattakar talauci a cikin al’umma, muddin babu ilimi to kuwa babu hangen nesa. Idan babu ilimi babu ci gaba, haka kuma in dai babu ilimi ba za ka iya cin galabar ayyukan da suke barazana ga sha’anin tsaro ba.”

A don haka shugaban na Najeriya ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da saka jari a bangaren ilimi domin gina al’ummar kasa.

Daga karshe shugaban ya gabatar da cekin kudi na rance a matsayin gwaji ga dalibai da aka zabo daga shiyoyin kasar, haka kuma ya mika wani cekin kudin ga shugabannin jami’ar Bayero ta Kano da kuma fasaha dake Owerri, wanda wannan shi ne alamun an kaddamar da shirin. (Garba Abdullahi Bagwai)