Firaministan Isra’ila ya ce matsa lambar aikin soja a Rafah zai taimaka ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2024-07-19 12:36:41 CMG Hausa
Ofishin firaministan kasar Isra’ila ya fitar da wata sanarwa jiya Alhamis, inda firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana Rafah a matsayin wuri mai matukar muhimmanci ga Hamas, inda Isra’ila ta kara matsawa Hamas lamba ta fuskar aikin soja, da bukatar ta yi iyakar kokarin sakin mutanen Isra’ila da take tsare da su, a matakin farko na tsagaita bude wuta. A cewar Netanyahu, irin wannan matsin lamba daga bangarori biyu, zai taimaka ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Rafah, birni ne mafi kudanci dake zirin Gaza, inda sojojin Isra’ila suka rika kaddamar da farmaki, abun da ya janyo karuwar asarar rayuka da wadanda suka ji rauni cikin sauri a kwanakin nan. Sabuwar kididdiga daga hukumar kula da kiwon lafiya a zirin Gaza dake Palesdinu ta nuna cewa, tun bayan barkewar sabon zagayen rikicin Palesdinu da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar da ta gabata kawo yanzu, matakan soja da Isra’ila ta kaddamar a zirin Gaza sun yi ajalin Palasdinawa sama da dubu 38, tare da jikkata wasu fiye da dubu 89. (Murtala Zhang)