logo

HAUSA

Sin ta samu sakamako da dama bisa matakan bude kofa ga waje da ta dauka

2024-07-19 18:13:07 CMG Hausa

Masu kallonmu, barka da war haka. Jiya Alhamis, an ba da sanarwa a cikakken zama na 3 na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20. Sanarwar ta nuna cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga waje, da kuma inganta aikin yin kwaskwarima ta hanyar bude kofa ga waje. Kana, ya kamata a karfafa aikin bude kofa ga waje ta hanyar habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen duniya bisa manyan kasuwannin da Sin take da su cikin kasa, yayin da kuma ake kafa sabon tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje.