Rukunin ‘yan JKS na NPC da na CPPCC sun gudanar da taro don kara fahimtar takardar cikakken zama na 3 na kwamitin kolin jam’iyyar karo na 20
2024-07-19 20:55:49 CMG Hausa
A yau ne, rukunin ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta Sin (ko JKS), na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC, sun gudanar da taro don koyon abubuwan da aka tanada cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun cikakken zama na 3 na kwamitin kolin jam’iyyar karo na 20, da takardar taron, da nazarin yadda za a dauki matakai a wannan fanni.
A gun taron, an yi nuni da cewa, an gudanar da cikakken zama na 3 na kwamitin kolin JKS karo na 20 a lokaci mai muhimmanci da ake kokarin sa kaimi ga raya kasa daga dukkan fannoni, da farfado da al’ummar kasar ta hanyar samun zamanintarwa irin ta kasar Sin. An tattauna, da zartas da kudurin kwamitin tsakiya na JKS game da yadda za a zurfafa yin kwaskwarima, da sa kaimi ga zamanintarwa irin ta kasar Sin, wanda ya tsara shirye-shirye a wannan fanni ta hanyar kimiyya, da tabbatar da abubuwan da za a yi gyare-gyare a kai da kuma yadda za a yi kwaskwarima, wannan ya shaida cewa, an yi la’akari da yadda za a cimma buri, da kuma yadda za a daidaita matsaloli, a matsayin sabbin manufofin da aka tsara na kara yin kwaskwarima a dukkan fannoni yayin da aka kama sabon tafarki. (Zainab Zhang)