logo

HAUSA

Kwamitin tsakiyar jami’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira taron ba mambobinsa ba

2024-07-19 14:47:44 CMG Hausa

 

Kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS ya kira taron wadanda ba mambobinsa ba a ran 20 ga watan Mayu a nan birnin Beijing, inda manyan shugabannin Sin suka saurari shawarar jagororin  mabambantan jami’yyun siyasa da shugabanin kungiyoyin masana’antu da kasuwanci da ma wakilan mutanen da ba su da alaka da jami’iyyu, kan aikin zamanintar da al’ummar Sin. Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS Xi Jinping ya halarci taron tare da ba da jawabi, inda ya ce, ofishin siyasa na kwamitin tsaskiyar JKS ya yanke shawarar kiran cikakkan zama karo na 3 na kwamitin tsakiyar JKS, da zummar nazarin tsarin zurfafa yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje a dukkan fannoni, da ma hanzarta zamanintar da al’ummar Sin da yanke shawara, bisa sabbin yanayi da ayyukan da ake fuskanta a sabon mataki. Kuma burin taron shi ne aiwatar da ruhin babban taro karo na 20 na JKS, da tsai da tsarin zurfafa yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje a dukkan fannoni, ta yadda za a samar da karfi da tabattattun tsare-tsare ga burin zamanintar da kasar Sin zuwa kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu yayin da jamhuriyar jama’ar kasar Sin ke cika shekaru 100 da kafuwa.

Zaunannen wakilan kwamitin tsakiyar JKS Wang Huning da Cai Qi da Ding Xuexiang su ma sun halarci taron. (Amina Xu)