Hadin gwiwar Sin da Afirka na bunkasa ci gaban masana’antun Afirka
2024-07-18 16:23:11 CMG Hausa
A cikin ‘yan shekarun nan, Sin da Afirka suna kara samun moriyar juna a hadin gwiwar bunkasa masana’antu, tare da samun sakamako mai kyau a tsakanin bangarorin biyu, sun kuma ci gaba da daukar sabbin matakai masu inganci kan hanyar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ta Sin da Afirka. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da yadda kasar Sin ke goyon bayan raya masana’antu a wasu kasashen Afirka uku, wato Kamaru, Uganda, da Zambia.