logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin na ci gaba da bunkasa daga dukkanin fannoni duk da sauye-sauye da ake fuskanta

2024-07-18 16:25:30 CMG Hausa

Tun a rabin farkon shekarar nan ta 2024, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kaso 5 bisa dari, wanda hakan ke nuni ga farfadowarsa bisa daidaito, duk kuwa da kalubalen da yake fuskanta a gida da ketare. Masharhanta da dama na ganin hakan shaida ce dake tabbatar da matsayin tattalin arzikin kasar Sin na kasancewa injin dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Ko shakka babu ana iya ganin sassa da suka haifar da wannan ci gaba. Musamman fannin fadadar cinikayya, wadda cikin rubu’in farko na bana ta bunkasa da kaso 6.1 bisa dari, sannan akwai fannin karuwar yawan hatsi da kasar ta samu a kakar bana. Ga kuma fannin sarrafa hajoji daga masana’antu ba tare da gurbata muhalli ba, da na bayar da hidimomi, da fannin kere-keren injuna masu sarrafa kansu, da fannin samar da sabbin makamashi, wadanda dukkanin suke karfafa bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin.

A daya hannun kuma, ana iya ganin yadda bukatun sayayya a cikin gida ke karuwa, yayin da bukatun hajoji daga ketare ma ke habaka, har ma wasu alkaluma suka nuna karuwar hajoji da hidimomin da kasar Sin ke samarwa ga ketare, sun samar da karin kaso 13.9 bisa dari na ci gaban tattalin arzikin kasar a rabin farko na shekarar nan.

A fannin samar da manufofi ma, gwamnatin Sin ta taka rawar gani wajen aiwatar da manufofi daban daban, wadanda ke ingiza ci gaba, da karfafa sayayya da kare sana’o’i.

A kan ce, “Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”. Tun daga rabin farko na shekarar bana, an ga ci gaba a fannonin bunkasar tattalin arzikin Sin bisa daidaito da karsashi, don haka ko shakka babu wannan ci gaba zai dore, karkashin karfin sashen sarrafa kayayyaki da bayar da hidimomi, da kyakkyawan yanayin zamantakewar al’umma. A daya bangaren kuma, kwazon da ake yi a fannin zurfafa gyare-gyare a dukkanin fannoni zai ci gaba da karfafa tushe, da samar da tabbaci ga cimma zamanintarwa irin ta kasar Sin. (Saminu Alhassan)