logo

HAUSA

Kwamitin kolin JKS ya amince da kudurin kara zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni

2024-07-18 19:42:43 CMG Hausa

Kwamitin kolin JKS na 20 ya amince da kudurin kara zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni, da nufin bunkasa zamanantarwa irin ta Sin. An amince da kudurin ne a cikakken zaman kwamitin na 3 da ya gudana tsakanin ranaikun Litinin zuwa Alhamis din nan.

Ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ne ya jagoranci zaman. Kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi, kamar dai yadda wata sanarwar bayan taron da aka fitar a yau Alhamis ta bayyana.

Yayin zaman, an saurari, tare da tattauna batutuwan da suke kunshe cikin wani rahoto kan ayyukan ofishin siyasa na kwamitin kolin karkashin jagorancin shugaba Xi, a madadin ofishin siyasar, tare da nazari, da amincewa da kudurin kwamitin kolin na JKS don gane da kara zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni, da nufin bunkasa zamanantarwa irin ta Sin. Shugaba Xi ya yi fashin baki don gane da sassan kudurin da aka amince da shi.

A cewar sanarwar bayan taron, makasudin zurfafa sauye-sauye daga dukkanin fannoni ya hada da ci gaba da kyautatawa, da bunkasa tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin, da zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin kasa, da karfafa kwarewar jagoranci.

Kaza lika, sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa shekarar 2035, za a kai ga gina managarcin tsarin raya tattalin arziki irin na gurguzu daga dukkanin fannoni, da kara inganta tsarin na gurguzu mai salon musamman na Sin, da zamanantar da daukacin tsarinmu, da ikon aiwatar da jagoranci, da cimma salon zamanantarwa na gurguzu".

Dukkanin wadannan za su kafa ginshiki mai karfi na gina kasar Sin, yadda za ta zama mai bin salon gurguzu na zamani a dukkanin fannoni nan zuwa tsakiyar karnin nan da muke ciki.

Za a kammala daukacin ayyukan sauye-sauyen da aka fayyace cikin kudurin ne nan zuwa lokacin bikin cikar jamhuriyar jama’ar kasar Sin shekaru 80 da kafuwa a shekarar 2029.  (Saminu  Alhassan)