logo

HAUSA

Aiwatar da shirin “kafa kasar Palasdinu da ta Isra’ila” ita ce hanya daya kadai da za ta iya magance rikicin yankin gabas ta tsakiya

2024-07-18 11:17:42 CMG Hausa

 

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya yi jawabi a wajen taron muhawara da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a jiya Laraba kan batun rikicin Palasdinu da Isra’ila, inda ya ce, tabbatar da ganin an aiwatar da shirin “kafa kasar Palasdinu da ta Isra’ila” ita ce hanya daya kadai da za ta iya magance aukuwar rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Fu Cong ya kara da cewa, rashin tabbatar da wannan shiri da kuma hana al’ummar Palasdinu ta kafa kasarsu, su ne musabbabin tsanantar yanayin dake tsakanin Palasdinu da Isra’ila a cikin dimbin shekarun da suka gabata. Ba a tabbata da ikon Falasdinawa na kafa kasarsu ba. Yankin Gaza yanki ne na Paladsdinu da na jama’arta. Kasar Sin na goyon bayan Palasdinawa da su kafa kasarsu mai ’yancin kai da kuma gudanar da harkokinsu da kansu. Fu ya kuma ba da shawarar cewa a kira taron wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa mafi girma a hukumance da zai kawo sakamako mafi yakini don tabbatar hakikanin lokaci da akidar aiwatar da wannan shiri.

Kazalika, Fu ya nuna cewa, tsagaita bude wuta nan da nan shi ne abin da aka sa gaba wajen ceton rayukan al’ummun fararen hula. Kuma aikin gaggawa a halin yanzu shi ne habaka hanyoyin shigar da tallafin jin kai da nufin sassauta rikicin jin kai mai tsanani da ake fuskanta a wurin. Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi hakuri da juriya don kaucewa daukar matakan da za su tsananta halin da ake ciki da ma hana barkewar wani babban rikicin dake da yiwuwar shafar duk fadin yankin gabas ta tsakiya gaba daya. Mr. Fu ya tabbatar da cewa, bangaren Sin zai yi namijin kokarin wajen kara yin hadin kai da mabambantan bangarori don taka rawar gani wajen kwantar da halin da ake ciki a yankin Gaza da sassauta rikicin jin kai da kuma tabbatar da ganin an aiwatar da wannan “shirin kafa kasashe biyu” a yankin. (Amina Xu)