Sin ta kaddamar da tallace-tallacen yawon bude ido na lokacin zafi don karfafa sayayya
2024-07-18 10:52:19 CMG Hausa
A jiya Laraba ne aka fara wani gangamin tallace-tallacen al’adu da yawon bude ido na hutun lokacin zafi a birnin Erdos, wani shahararren wurin yawon bude ido a yankin Mongoliya ta gida da ke arewacin kasar Sin.
Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar wacce ta shirya gangamin ta ce, za a gudanar da ayyuka kusan 37,000 a fadin kasar don inganta al'adu da sha'anin yawon bude ido, tare da yayata sabbin yanayin sayayya da kuma manufofi masu fifiko.
Ta kara da cewa, gangamin zai kunshi ayyukan yawon bude ido da dama, wadanda suka hada da yawon shakatawa na dare da tafiye-tafiyen karin ilimi, kuma za a tanadi matakan ingiza biyan bukatu kamar takardun rangwamen farashi da tikitin farashi mai rahusa a wurin don ingiza damar yin sayayya.
Hutun lokacin zafi da ke gudana a watan Yuli da Agusta na kowace shekara shi ne kololuwar lokaci na yawon shakatawa na cikin gida, musamman a tsakanin iyalai da yara. Rahoton da Ctrip mai ba da hidimar tafiye-tafiye ta yanar gizo ya fitar, ya nuna armashi a kasuwar yawon bude ido ta cikin gida ta kasar Sin a bana, inda adadin dake neman otal-otal da tikitin jirgin sama ta intanet ya karu da sama da kashi 20 cikin dari bisa shekarar bara. (Yahaya)