Sin ta dakatar da tattaunawa da Amurka kan dakile makamai da hana yaduwar makamai a sabon zagaye
2024-07-17 20:10:47 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin ta dakatar da tattaunawa da kasar Amurka kan dakile makamai da hana yaduwar makamai a sabon zagaye, bisa gazawar Amurka ta aiwatar da matakan da suka dace.
A watan Nuwamban shekarar 2023, Sin da Amurka sun gudanar da irin wannan tattaunawa a birnin Washington dake Amurka. Bayan hakan, wasu manyan jami’an Amurka sun zargi kasar Sin da kin shiga tattaunawar a sabon zagaye tare da Amurkan, kuma Sin ba ta bayyana ra’ayi kan shawarar Amurka game da batun ba.
Game da hakan, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kiyaye mu’amala tare da Amurka, kan batun dakile makamai na kasa da kasa, bisa tushen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa, da kuma cimma moriyar juna. Amma tilas ne Amurka ta girmama babbar moriyar kasar Sin, da samar da yanayi mai kyau na yin shawarwari a tsakanin bangarorin biyu.
Ban da wannan kuma, Lin Jian ya bayyana cewa, Amurka ta yada jita-jita, da zargi game da yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Sin ba tare da sahihin dalili ba, da daukar matakan sanya tarnaki ga wasu jami’an kasar Sin kan takardar Biza, wanda hakan tsoma baki ne cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, kana ya sabawa dokokin kasa da kasa, da ka’idojin raya huldar dake tsakanin kasa da kasa, don haka Sin ta nuna adawarta, kana ta riga ta gabatar da korafinta kan hakan ga Amurka. (Zainab Zhang)