Rukunin motocin watsa shirye-shirye kai tsaye na CMG sun isa Stade de France gabanin bude gasar Olympic ta Paris
2024-07-17 20:42:13 CMG Hausa
Jerin gwanon motocin watsa shirye-shirye kai tsaye guda 6, masu aiki da fasahohin 8K/ UHD na kafar CMG ta kasar Sin, sun isa babban filin wasa na Stade de France dake birnin Paris na Faransa, gabanin bude gasar Olympic nan da ‘yan kwanaki.
Motocin dai na shirye-shiryen gabatar da gasar kai tsaye ga sassan duniya, bisa fasahohin zamani mafiya nagartar fitar da hotuna da muryoyi daga wurin da ake gudanar da gasar ta Olympic, da sauran ayyukan gasar da suka hada da bikin rufewa. Da wannan sakamako, gasar Olympic ta Paris ta shekarar 2024, za ta kasance gasar Olympic ta lokacin zafi ta farko, wadda za a yada ta amfani da fasahohin 8K/UHD.
A matsayin CMG na babbar kafar watsa shirye-shirye ga sassan kasa da kasa, wadda kuma ke da izinin watsa gasar ta Olympic ta Paris, kafar ta shirya gabatar da shirye-shirye mafiya kayatarwa, sama da gasannin Olympic da ta taba watsawa kawo yanzu. (Saminu Alhassan)