Kwararru na neman bunkasa makamashin zafin karkashin kasa a Afirka
2024-07-17 10:05:47 CMG Hausa
A jiya Talata ne kwararru suka fara wani taro na kwanaki biyu a Nairobi, babban birnin Kenya, domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen gaggauta bunkasa makamashin zafin karkashin kasa wato Geothermal a Afirka.
Taron ya tattaro masana, masu tsara manufofi, masu samar da kudade, da masu zuba jari a fannin makamashin zafin karkashin kasa daga kasashe 20 na Afirka, don inganta amfani da makamashi da ake sabuntawa a Afirka.
Babban sakataren ma’aikatar makamashi ta kasar Kenya, Alex Wachira ya ce, a halin yanzu kasar na samar da wutar lantarki kimanin megawatt 985 daga makamashin zafin karkashin kasa.
Joseph Mwangi, manajan ayyuka na cibiyar kawar da hatsarin makamashin zafin karkashin kasa na yankin gabashin Afirka (GRMF), ya bayyana cewa, yayin da nahiyar ta rumgumi tsarin zirga-zirga da ababen hawa masu amfani da lantarki don kawar da hayakin carbon a fannin sufuri, makamashin zafin karkashin kasa zai taka muhimmiyar rawa wajen saukaka wannan sauyin.
Gregory Gamula, daraktan tsare-tsare da bunkasuwa na kamfanin samar da wutar lantarki na Malawi, ya ce a shirye kasarsa take ta raba kafa kan makamashin da take samu ta hanyar amfani da albarkatun makamashin zafin karkashin kasa. Ya ce, Malawi na tattaunawa da masu zuba jari don kafa tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 10 ta makamashin zafin karkashin kasa cikin matsakaicin lokaci. (Yahaya)