WTO ta kira taron tattaunawa kan manufofin cinikin kasar Sin a Geneva
2024-07-17 13:59:45 CMG Hausa
WTO ta kira taron tattaunawa kan manufofin cinikin Sin jiya Talata a Geneva na Switzerland, taron mai taken “Fahimtar manufofin cinikin Sin daga kwamitin tsakiya zuwa gwamnatocin wurare”, na da zummar taimakawa mambobin WTO da su fahimci manufofin Sin a bangaren ciniki.
Masana daga hukumomin nazari da jami’o’i da wakilan kamfanoni masu jarin waje dake kasar Sin sun yi bayani kan manufofi da tsare-tsare da dabarun ayyukan gwaji da Sin take yi don tabbatar da samun bunkasuwa mai inganci da habaka bude kofa ga waje, kuma sun yi cudanya da mu’ammala da mahalarta taron daga ofishin sakantaren WTO da mambobin WTO da kungiyoyin kasa da kasa da kafofin yada labarai.
Masana mahalarta taron sun nazarci yanayin tattalin arziki da hangen nesa kan makomarsa bisa hakikanin halin da ake ciki, kuma sun yi bayani kan sabbin manufofin da Sin take fitar wajen raya sabon karfi na samar da hajoji da hidimomi masu karko da kafa kasuwar bai daya a duk fadin kasar da ma habaka karfin kamfanoni masu zaman kansu da dai sauransu. Dadin dadawa, masana mahalarta taron da wakilan kamfanoni sun yi bayanai masu zurfi kan manufofin Sin na habaka yankunan gwajin bude kofa ga waje na sana’ar ba da hidima da ci gaban da Sin take samu wajen kyautata yanayin cinikayya da samar wa ’yan kasuwa baki sauki wajen gudanar da harkokinsu a nan kasar Sin, bisa hakikanin ayyuka da manufofi da Sin ta tsara, ta yadda za a iya tabbatar da ganin baki ’yan kasuwa sun samu riba a kasar Sin. (Amina Xu)