logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara baiwa jihohin kasar buhunan shinkafa domin rabawa kyauta ga al’umominsu

2024-07-17 09:03:16 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta raba motoci 740 dauke da buhunan shinkafa ga jihohin kasar 36, ciki har da birnin Abuja domin rabawa al’umma a wani mataki na rage matsin rayuwa da ake ciki a kasar.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin 15 ga wata jim kadan da kammala taron majalissar zartarwar kasar a birnin Abuja, ministan yada labarai da wayar da kai Alhaji Muhammad Idris ya ce, kowacce jiha za ta rabauta da tirela 20 na shinkafa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Alhaji Muhammed Idris ya kara da cewa, kowacce mota tana dauke da buhuna 1,200 ne na  shinkafa mai nauyin kilogram 25.

Ministan ya ci gaba da cewa, ana sa ran gwamnonin jihohi za su sanya ido sosai wajen tabbatar da ganin cewar, masu rauni a cikin al’umma ne kawai za su amfana da shinkafar da aka samar a jihohinsu.

Baya ga wannan mataki ma, ministan ya ce, gwamnati tana daukar wasu matakai na daban da za su tabbatar da ganin halin matsin da ’yan Najeriya ke ciki yana raguwa sannu a hankali.

“Gwamnati za ta ci gaba da yin duk abun da ya kamata wajen tabbatar da ganin ’yan Najeriya suna da wadataccen abun da za su ci.”

Ministan yada labarai na tarayyar Najeriya ya kara nanata cewar, a yanzu haka gwamnati na bayar da tallafi mai yawan gaske ga bangaren noma domin kara kaimi wajen noma abinci don amfanin gida da kuma sayarwa ga kasashen waje. (Garba Abdullahi Bagwai)