logo

HAUSA

Sin ta nemi NATO da ta waiwayi kura-kuren da ta aikata a baya

2024-07-17 13:54:15 CMG Hausa

 

Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da muhawar game da doka da odar kasa da kasa da hadin kai tsakanin mabambanta bangarori a jiya Talata, inda wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya gabatar da jawabi cewa, yanzu ana fuskantar matsalar dambarwar siyasar kasa da kasa da kin dunkulewar duniya a fannin tattalin arzikin kasa da kasa da ma gudanar da harkokin kasa da kasa a kebantattun rukunoni, hakan ya sa Bil Adam na sake fuskantar matsalar zabar hanyar da ta dace. Sin na kalubalantar NATO da wasu kasashe da su sake waiwayar kura-kuren da suka aikata a baya, kada su zama masu samun moriya ta hanyar keta moriyar sauran, da masu illata yanayin tsaron duniya baki daya.

A cewarsa, yanzu ana fuskantar matukar rudani, ana samun mabambantan ra’ayoyi yayin tattaunawa game da doka da odar kasa da kasa. A hakika dai, wasu kasashen dake daukar matsayin doka da oda bisa tushen ka’ida da suka tanada, suna da zummar kirkira wata tsari na daban, don tabbatar da ra’ayin ma’auni biyu da kasancewa kan matsayi na musamman.

Fu Cong ya kara da cewa, doka da oda daya kacal a duniya ake amincewa da ita, wato doka da oda bisa tushen dokar kasa da kasa. Kuma tsari daya kadai ake bi, wato ka’ida mai tushe na huldar kasa da kasa bisa hurumin tsarin mulkin MDD. (Amina Xu)