logo

HAUSA

Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Bunkasa Kamar Yadda Ake Fata

2024-07-17 07:46:16 CMG Hausa

A rabin farko na wannan shekara, karkashin jagorancin babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS wato komarade Xi Jinping, dukkan yankuna da sassan kasar Sin sun aiwatar da shawarwari da tsare-tsare da kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suka zayyana. An bi ka'idar neman ci gaba tare da tabbatar da zaman lafiya, da inganta zaman lafiya ta hanyar ci gaba da kafa sabbin manufofi kafin kawar da tsofaffin manufofi, tare kuma da aiwatar dasu yadda kamata. Sakamakon haka, tattalin arzikin kasar gabadaya ya kasance cikin karko da armashi, wanda ke nuna ci gaba mai karfi a fannin samar da hajoji, da wadata a fannin bukatu, da daidaito a bangaren farashi da aikin yi, da ci gaba da habaka kudin shiga na kowane mutum, ta hanyar bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko. Alkaluman hukumar kididdaga ta kasar (NBS) sun nuna a ranar Litinin cewa, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kashi 5 cikin dari a rabin farko na shekarar 2024, idan aka kwatanta da makamacin lokacin a bara, wanda hakan yayi daidai da hasashen da mahukunta suka yi, kuma yake nuni da cewa tattalin arzikin Sin na bunkasa kamar yadda ake fata.  

\GDPn kasar Sin ya kai kusan Yuan tiriliyan 61.68 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 8.65 a watanni shidan farkon shekarar kamar yadda alkaluman NBS suka nuna. Kudin shiga na kowane mutum bayan haraji na kasar Sin a watanni shidan farkon shekarar ya kai Yuan 20,733 kwatankwacin dalar Amurka 2,907.32. Alkaluman kwastam sun cewa, cinikayyar waje na kasar Sin ya kai wani sabon matsayi a cikin wadannan watanni 6 na farko, inda yawan cinikin kayayyaki ya karu da kashi 6.1 cikin dari zuwa Yuan triliyan 21.17 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.97. Aikin fitar da kayayyaki ya ci gaba da bunkasuwa, ya kuma karu da kashi 6.9 cikin 100. Kana yawan kudaden da aka samu daga bangaren kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabo yayin da aka samu bunkasuwa sosai a fannonin hidima, da nishadi da tafiye tafiye, da yawon shakatawa da ayyukan al’adu da fasaha.

Yayin da yake tabbatar da ci gaban da aka samu, firaministan kasar Sin Li Qiang ya kuma jaddada bukatar tsaftace tunani. Ya ce, abubuwan da suka shafi ci gaban da aka samu sun kasance masu sarkakiya fiye da da, don haka magance wadannan matsaloli masu wuyar gaske wajen gudanar da harkokin tattalin arziki na bukatar kokari sosai, saboda a halin yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar wani yanayi mai sarkakiya da tsanani daga waje. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)